fidelitybank

Sai an biya miliyan 200 kafin mu saki shugaban PDP na Legas – ‘Yan bindiga

Date:

Jam’iyyar PDP reshen jihar Legas, ta yi kira ga jami’an tsaro da hukumomin gwamnati da su sa baki cikin gaggawa domin ganin an sako shugabanta Philip Aivoji da aka sace.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP reshen jihar Legas, Hakeem Amode, ya yi wannan kiran nea wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce, An sace Aivoji ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu da misalin karfe 6:00 na yamma a hanyar Legas zuwa Ibadan a lokacin da yake dawowa daga taron masu ruwa da tsaki a jihar Oyo da Gwamna Seyi Makinde da Gwamna Ademola Adeleke na Osun.

Ya ce, abin takaici ne yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a kasar nan.

Sace Aivoji na nuna matukar bukatar daukar kwararan matakai daga gwamnati da masu ruwa da tsaki don kawar da wannan matsalar.

Ya kara da cewar, suna kira ga gwamnatocin jihohin Oyo, Ogun, da Legas, tare da jami’an tsaro, da su kara kaimi wajen ganin an dawo da shi lafiya ga iyalansa.

Kakakin jam’iyyar PDP ya ce idan aka kara kokarin jami’an tsaro za a ceto Aivoji daga hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni na cewa ‘yan bindigar sun nemi a biya Naira miliyan 200 kafin su sako shugaban jam’iyyar Phi;ip Aivoji.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp