Kasar Singapore ta rataye wasu mutane biyu bisa laifin safarar miyagun kwayoyi, a wani mataki da masu rajin kare hakkin bil adama suka yi Allah wadai da shi.
Daya daga cikin mutanen da aka yankewa hukuncin dan kasar Singapore ne, dayan kuma dan kasar Maleshiya makwafciyar kasar ne.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar ta zartar da hukuncin kisa ga mutane hudu a cikin ‘yan watannin da suka gabata bayan hutun shekaru biyu da aka yi na zartar da hukuncin kisa.
Kwanan nan ministan harkokin cikin gida na kasar Singapore K. Shanmugamya shaida wa BBC cewa ko shakka babu hukuncin kisa ya taimaka wajen hana fasa-kwaurin kwayoyi.
Amma kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce shaidusun nuna cewa hakan ba shi da tasiri.
Ta kira hukuncin kisa a matsayin ‘abin kunya da rashin mutuntaka’.