Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded ta Spain, Sadiq Umar da ɗanmajalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta arewa, Bello El-Rufai sun haɗa hannu domin mallakar ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna.
Ƙungiyar Rancher Bees, daɗaɗɗiyar ƙungiya ce mai tarihi a jihar Kaduna, da ta yi tashe a arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya a shekarun baya, amma sai ta samu koma-baya, har aka daina maganarta.
A wata sanarwa da ya fitar, Sadiq Umar ya bayyana farin cikinsa kan mallakar ƙungiyar, wadda ya ce za su iya ƙoƙarinsu domin dawo da martabarta.
Ya ce, “zan haɗa hannu da Bello El-Rufai domin dawo da martabar ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna. Na taso ina kallon ƙungiyar nan, wadda ta fitar da zaratan ƴanƙwallo da suka yi fice a duniya. Wannan abun farin ciki ne a gare mu,” in ji Sadiq Umar.
Ya ce babban burinsu shi ne ganin ƙungiyar ta koma gasar firimiyar Najeriya, “ina farin cikin irin murnar da na ga magoya bayan ƙungiyar sun fara nunawa da ma mutanen Kaduna. Za mu dawo da harkokin wasa sosai a Kaduna,” in ji Sadiq.
A nasa ɓangaren, Bello El-Rufai ya ce yana farin cikin sa hannu a yunƙurin dawo da martabar ƙungiyar, lamarin da ya ce zai yi iya ƙoƙarinsa domin samun nasara,