Baya ga buga kwallon kafa, akwai wasu ‘yan wasan da suka yi suna wajen kyauta da yin alheri ga kasashen su.
Sadio Mane ya na cikin wannan jeri, saboda yadda ya ke taimakawa al’ummar kasarsa ta Senegal.
Haka zalika akwai Mesut Ozil wanda dubunnan marasa karfi su ke samun abinci a sanadiyyarsa.
An san mafi ‘yan wasan kwallon kafa da rayuwa cikin daula da facaka da dukiya, saboda irin albashin da suke samu, amma ba duk a ka zama daya ba.
A wannan rahoto da muka tsakuro daga Sportszion da Sportmob, mun kawo wasu ‘yan kwallon da suke amfani da dukiyarsu wajen taimakawa al’umma.
1. Sadio Mane Wanda muka fara da shi a jerin na mu shi ne Sadio Mane. Kwanaki baya CNN ta rawaito cewa, dan wasan na Liverpool ya bada dala dubu 693,000 wajen gina asibiti.
Sadio Mane ya bada wadannan kudi ne domin a gina asibiti a kauyensu na Bambali a Sanagal. Baya ga haka akwai ayyukan alherin da yake yi a kasarsa.
2. Tsohon dan wasan Arsenal da Real Madrid, Mesut Ozil, ya dade ya na taimakawa gajiyayyu da marasa hali, kuma ya kan yi magana idan ya ga a na zalunci. Bayan ya lashe gasar kofin Duniya, Mesut ya bada kyautar kudin da ya samu, domin ayi wa wasu magani. Tauraron ya yi fice wajen dawainiyar marasa lafiya.
3. Lionel Messi Lionel Messi ya tashi ne a kasar Argentina a halin da babu yabo babu fallasa. Har yanzu bai manta da tushensa, ‘dan wasan yana cikin masu taimakawa mutane. Gidauniyar Leo Messi Foundation ta na kokari wajen taimakawa marasa karfi da ilmin boko da kula da lafiyarsu, sannan kuma Messi jakada ne na
4. Neymar Jr. Neymar yana cikin ‘yan kwallon da suka fi kowa albashi a Duniya, sannan kuma yana cikin wadanda suke taimakawa al’umma daidai bakin gwargwado. Akwai wani kokari da ‘dan wasan na PSG ya sa a gaba watau “Waves for Water” domin samar da ruwan sha ga mutanen Brazil baya ga sauran alherin da yake yi.
5. Cristiano Ronaldo Rahoton Sport Mob ya nuna Cristiano Ronaldo ya na cikin ‘yan kwallon da suka yi fice wajen yin kyauta, hakan ta sa ya taba lashe kyautar “Athletes Gone Good Award”. Ronaldo ya taba biyan $83,000, domin ayi wa wani karamin yaro magani.
A 2012 ‘dan wasan ya tara kusan Dala miliyan biyu domin a taimakawa mutanen yankin Gaza.
6. Mario Balotelli Babban abin mamakin wannan jeri shi ne Mario Balotelli wanda aka sani da rashin da’a. Rabin kudin ‘dan wasan su na karewa ne wajen taimakawa ‘Yan Afrika.
A jerin na mu akwai ‘yan wasa irinsu Jermain Defoe wanda gidauniyarsa ta Jermain Defoe Foundation ta ke taimakawa Bayin Allah da-dama a kasar Birtaniya. Haka zalika ‘dan wasan tsakiyar nan, Gareth Barry ya na taimakawa wadanda ba su da karfi. A cikin wadanda suka yi ritaya akwai Didier Drogba da Nnwanko Kanu.