fidelitybank

Sace daliban makaranta da ‘yan gudun hijira ya nuna gazawar Tinubu – Amnesty

Date:

Ƙungiyar Amnesty International ta ce sace fiye da ƴan gudun hijira a jihar Borno da ɗalibai ɗari biyu da tamanin da bakwai da malamai a yankin Kuriga a jihar Kaduna na nuna gazawar hukumomin Najeriya na kare al’umma daga hare-haren ƴan bindiga da suka kashe dubban ƴan ƙasar cikin shekara biyar da ta gabata.

Ƙungiyar, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a ta hannun shugabanta a Najeriya, Isa Sanusi, ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da mutanen da aka sace domin haɗa su da iyalansu.

A cewar ƙungiyar, dole ne hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yawaitar sace-sacen da ake yi a sassa da dama na Najeriya tare da gabatar da sakamakon binciken ga al’umma sannan su tabbatar an hukunta waɗanda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.

Amnesty ta ce, “sace-sacen mutane da dama a baya-bayan nan ƙarara sun nuna cewa shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa ba su da tsayayyen tsari na kawo ƙarshen miyagun laifukan ƴan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a sassan jihohin Najeriya. Duk matakan tsaron da shugaba Tinubu da gwamnatinsa ke aiwatarwa ba sa tasiri,” in ji Isa Sanusi.

“Ganin yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a Najeriya a yanzu, a bayyane take cewa batun kare rayuwa da dukiyoyin al’umma ya na ƙasa cikin jerin abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Bai kamata a ƙyale mutane su zauna cikin fargaba da tsoron hari da garkuwa ba.

Yawan gazawar hukumomin Najeriya wajen kare mutane abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba kuma dole ne a kawo ƙarshen sa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Amnesty ta kuma yi kira da a tabbatar da waɗanda ke da nauyin samar da tsaro a yankunan da aka yi sace-sacen jama’a su yi bayani kan gazawar da ta jefa rayuwar ɗaruruwan mutane cikin haɗari.

A ranar Alhamis ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kan wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna inda suka sace ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, sai dai malamin ya samu kuɓuta sai kuma ɗalibi guda da ya mutu.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp