Mali ta dakatar da bayar da bisa ga ƴan ƙasar Faransa, a ofishin jakadancinta da ke birnin Paris da kuma ma’aikatar harkokin waje.
Wata sanarwa daga ƙasar ta ce matakin na ramuwar gayya ne, kan ayyana Mali cikin yankunan da ke da hatsarin shiga.
“Mun yi mamakin yadda Faransa ta ayyana Mali a cikin yankunan da ke da hatsarin shiga”.
A farkon makon nan Faransa ta dakatar da bayar da bisa ga ƴan Mali, ta kuma rufe ofishinta na bayar da bisa da ke Bamako babban birnin Mali.
Dambarwa tsakanin ƙasashen biyu ta samo asali ne daga juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaban Nijar Mohamed Bazoum, makonni biyu da suka wuce.
Gwamnatocin mulkin soji a Mali da Burkina Faso da kuma Guinea duk sun bayyana goyon bayan su ga juyin mulkin, kuma sun yi gargaɗi kan ɗaukar matakin soji kan dakarun da suka kifar da gwamnati a Nijar.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Mali da Faransa bayan dakarun Malin sun yi juyin mulki a 2020 da kuma 2021.