Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya taya shugaban Cocin Christ Holy Church (Odozi-Obodo), Archbishop, Daniel Okoh, murnar zabensa da aka yi masa a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
A cikin wata wasika da ya sanya wa hannu, Kwankwaso ya bayyana zaben Okoh a matsayin wanda ya fi kowa cancanta.
“Mun ma fi jin dadin yadda tsarin zaben da aka gudanar ya samar da Shugaban, wanda fitaccen malami ne, dan kishin kasa, jarumin tattaunawa tsakanin addinai tare da tarihin duniya wajen sasanta mutane, musamman ma mabiya addinai daban-daban, kuma mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya,hadin kai da bin doka da oda.
“Babu shakka kasarmu za ta zama wuri mafi kyau idan dukkan bayin Allah na kowane addini suka kusanci aikin makiyaya tare da juriya, tausayawa da aminci ga manyan tsare-tsare da kuka nuna a ofisoshi daban-daban da kuka mamaye a baya. Kuma a yau, yayin da kuka hau kan kujerar shugabancin CAN, fa’idar ta kara fadada, an kuma fadada hangen nesa; kuma addu’ar mu ce, a sabon matsayinku, Allah Madaukakin Sarki ya yi amfani da ku, da ikon Alherinsa, don yin nasiha da kuma motsa al’ummar Kiristanci ta Najeriya zuwa ga zurfin fahimtar juna, zuwa ga tattaunawa ta tausayawa da sauran, da kuma gina wata manufa ta daban, zumunci na gaske da kowa.