Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Bunu ya karbi mukamin sabon shugaban ‘yan sanda a jihar.
Bunu ya leka shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar, inda ya yi kira ga ‘yan jarida da ke aiki a jihar da su ba shi cikakken goyon baya don gudanar da ayyukansa na tsarin mulki cikin jajircewa.
An gabatar da sabon kwamishinan ne da manyan jami’an ‘yan sanda a jihar, bayan sun shiga ganawar sirri da suka dauki tsawon sa’o’i da dama.
Ku tuna cewa a makon da ya gabata ne aka tura Mohammed Bunu jihar Zamfara domin karbar Kolo Yusuf a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda.