Tsohon dan wasan Manchester United da Arsenal, Robin van Persie, ya goyi bayan kocin Liverpool Arne Slot ya yi nasara a aikinsa bayan ya maye gurbin Jurgen Klopp.
An nada Slot a matsayin sabon kocin Liverpool a farkon wannan makon.
Dan kasar Holland mai shekaru 45 ya bar aikinsa a Feyenoord, inda ya zauna na tsawon shekaru uku.
Da yake magana da ESPN Nederland, Van Persie ya ce game da Slot:
“Ina tsammanin (zai tafi) sosai. Yadda yake son buga wasa ya dace da salon wasan Klopp da abin da suka saba da shi a can.
“Ina tsammanin za su yi kyau sosai. Liverpool na ɗaya daga cikin mafi kyawun kulab a Ingila. Na sami damar buga wasa a wasu kungiyoyi biyu masu kyau sosai.”