Sabon gwamnan riko na jihar Ribas, Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya ya isa jihar, biyo bayan nadin da shugaban kasa Bola Tinubu yayi a ranar Talata.
Shugaba Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya dauki matakin tsawaita rikicin siyasar da aka dade a jihar, sannan ya kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakin gwamna Ngozi Nma Ordu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas.
Dakatarwar ta janyo suka daga manyan jiga-jigan siyasa da kungiyoyi da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da kungiyar kwadago da kungiyar lauyoyi ta kasa da dai sauransu.