fidelitybank

Sabon fim din Sharukh Khan Pathaan ya tayar da kura

Date:

Fim din da fitaccen jarumin fina-finan India na Bollywood Shahrukh Khan,ya yi na baya bayan nan wato Pathaan da za a sakI a mako mai zuwa ya zamo abin tattaunawa duba da irin hasashen da ake zai dauki hankali.

Tun bayan da aka saki tallan fim din mutane ke ta magana a akai kasancewa jarumin ya kwana biyu bai fito a fim ba, kamar yadda BBC ta rawaito. Shahrukh Khan, wanda jarumi ne da ake son shi ba a kasarsa ta India ba, har ma da sauran kasashen duniya, ya shafe shekaru hudu bai fito a fim ba sai a 2023. Jarumin mai shekaru 57 da haihuwa, ya fito da karfinsa a wannan karon a fim din Pathaan bayan a baya ya yi fina-finan da ba su yi wani fice ba.

Ana ganin irin abubuwan da suka faru da jarumin a baya kamar batun kama babban dansa Aryan, inda aka tuhumeshi da ta’ammali da kwayoyi ya janyo masa koma a fina-finan da ya yi a lokutan. Sabon fim din sa na Pathaan, ya kunshi manyan jarumai kamar Deepika Padukone da kuma John Abraham.

A yanzu ba a kasar India ba kadai, har ma da wasu kasashen duniya babu zance da ake a game da fina-finan Bollywood kamar fim din Pathaan, mutane jira suke kawai a sake shi. An kiyasta cewa tun da aka saki tallan fim din a makon da ya wuce, mutane miliyan 49 sun kalleshi a shafin YouTube, haka ma a shafin Tiwita ana ta magana a kansa.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp