Rahotanni na cewa tuni sabon farashin mai ya fara aiki a wasu gidajen mai mallakar kamfanin mai na Najeriya, NNPCL a Abuja ya nuna yadda ake sayar da man a kan sabon farashi na naira 1,030 kowacce lita saɓanin yadda ake sayar da shi a baya naira 897 kowacce lita.
Ƙarin na kimanin kaso 15, shi ne na biyu a tsawon wata guda.
Wannan dai na zuwa ne bayan bayanan da suka nuna kamfanin na NNPCL ya zare hannunsa daga dillancin man kamfanin Ɗangote, wani abu da ya nuna cewa akwai yiwuwar farashin man ya ƙara tashi.
Zare hannun NNPCL daga dillanci dai na nufin kamfanin ya daina cikasa giɓin da ake samu ko kuma tallafi na naira 133.
Wakilin BBC, Aminu Kutama ya ce daga zagayen da ya yi a Abuja cewa ana sayar da man a wasu gidajen man ƴankasuwa daga naira 1,040 zuwa sama