Jamâiyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce ya daina amfani da shafukan sada zumunta.
Tinubu ya bayyana cewa kusan ya kamu da cutar hawan jini a duk lokacin da ya yi amfani da shafukan sada zumunta.
Ya koka da yadda masu amfani da shafukan sada zumunta ke cin zarafinsa, don haka ya kauce ma hakan.
Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar APC ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da daya daga cikin abokansa, Ademola Oshodi ya wallafa a shafin Twitter.
A cikin faifan bidiyon, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce, yakan yi fushi a duk lokacin da ya karanta abubuwan da aka rubuta game da shi a shafukan sada zumunta.
âBa na kara karanta kafafen sada zumunta; suna ban takaici idan na karanta, nakan sami hawan jini da fushi.
âBa na karanta shi, don haka idan ina son jin wani abu; âyaâyana ko maâaikata na za su fadi wannan maganar, idan na gaji na ce don Allah a manta da shi,â inji Tinubu.
Tun bayan fitowar sa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar APC, Tinubu ya fuskanci cece-kuce.
Sai dai ya yi watsi da dukkan zarge-zargen da ya bayyana a matsayin karya da rashin tushe.