fidelitybank

Sabon Birni: Yan Bindiga sun budewa motar matafiya wuta

Date:

‘Yan bindiga sun kona matafiya kimanin mutum 42 a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Matafiyan wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa wurare daban-daban na kasar nan, domin kaucewa matsalar tsaro da ta addabi yankunansu.

Shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa lamarin ya afku ne a daren Litinin da misalin karfe 9 na safe. 7 daga cikin matafiyan ne kawai suka tsira, inda su na kwance a asibiti suna karbar magani.

Lamarin ya faru ne a wani kauye mai suna Teke a yankin Gidan Bawa na Karamar Hukumar Sabon Birni. Inda ‘yan bindigar suka bude musu wuta, domin tsayar da motar, wanda hakan ya yi sanadiyar juyawar motar,nan ta ke ta kama da wuta.

Sai dai hukumomin jihar Sokoto basu ce komi ba kan faruwar lamarin, yayin da ayyukan ta’addanci na ‘yan bindigar ke kara ta’azzara musamman a yankin Sabon Birni dake jihar Sokoto da yankin karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara, wanda ko a makon da ya gabata ‘yan bindigar sun shafe kwanaki suna cin-karensu ba-babbaka a hanyar Shinkafin. Inji Leadership.

 

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp