Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin ministoci bakwai da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike mata domin tantancewa.
A yau Laraba ne majalisar ta yi zaman tantancewar bayan an fasa yin sa a ranar Talata.
Majalisar ta jingine jadawalin ayyukanta na yau ɗin domin tantance su cikin sauri.
An fara ne da Nentawe Yilwatda, wanda zai maye gurbin Betta Edu a matsayin ministan ma’aikatar agaji da yaƙi da talauci.
Daga baya kuma aka tantance sauran kamar haka:
- Bianca Odumegu-Ojukwu – ƙaramar ministar harkokin waje
- Maigari Dingyadi – ministan ƙwadago da aikin yi
- Jumoke Oduwole – ministar ma’aikatu
- Idi Maiha – ministan ma’aikatar dabbobi
- Yusuf Ata – ƙaramin ministan gidaje
- Sauwaiba Ahmad – ƙaramar ministar ilimi.