Shugaban sojojin hayar Wagner, Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama, tare da ƙarin mutum tara a cikin jiragen sama a Rasha.
Rahotanni na cewa, yana cikin jirgin da kuma mutane tara.
A baya dai ya yi wa shugaban Rasha Vladimir Putin tawaye a kan yakin da suke yi da Ukraine.
Sai dai a cikin satin nan ne aka hangi wani faifan bidiyon da ya wallafa, bayan ya sauka a kasar Mali.


