Sama da gidaje 1,000 da gine-ginen kasuwanni da majami’u 11 da masallatai 11 ne ruwa ya rushe su, sakamakon mamakon ruwan sama da ya afku a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Wani mazaunin garin Kasuwar Magani, Tanko Gajere ya tabbatar wa da manema labarai a yau.
Ya bayyana cewa ruwan sama ya faro ne da yammacin ranar Alhamis da misalin karfe 6:30 na yamma kuma ya kwashe sama da sa’o’i uku, inda sama da iyalai 400 a yankin suka rasa gidajensu.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna da su aike da kayan agaji domin rage radadin iftila’in.
Tun dai a baya hukumar kula da yanayi ta kasa NIMET, ta yi gargadin cewa za a yi ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin kasar nan.