Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Peter Obi, ɗantakarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023.
An shirya tattakin ne domin yin bikin murnar cika shekara 64 da haihuwar Mista Obi.
Mai magana da yawun rundunar DSP Mansir Hassan ya ce bayanai sun nuna cewa akwai wasu “miyagu da ke shirin fakewa da gangamin domin haddasa fitina” a jihar.
DSP ya ce rundunar ta dakatar da duk wani taron jama’a mai kama da na siyasa har sai “lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓe a hukumance kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa Inec ta tsara”.
A cewar sanarwar: “Yayin da ake gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyu a ranar da magoya bayan Obi suka tsara gangamin, rundunar ‘yansandan Kaduna na ganin hakan zai haddasa rikici a wuraren da za a yi zaɓukan, abin da zai jawo rashin doka da oda a jihar.”
Rundunar ta kuma ci alwashin ɗaukar matakin shari’a kan duk wanda ya ƙi bin umarnin dakatar da gangamin siyasar.