Jami’an tsaron, NSCDC, sun tarwatsa wasu gungun mutanen da ake zargin ana karbar cin hanci a tashar Mobil, daura da makarantar St. Michael da ke unguwar Ajilosun a Ado-Ekiti dake jihar Ekiti.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, wanda ya sa ido kan yadda za a kada kuri’a a fadin jihar, ya lura da dimbin jama’a da tawagar jami’an NSCDC karkashin jagorancin mukaddashin kwamanda, Haruna Muhammed, ke tarwatsa jama’a.
Mista Musa Faruk, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan siyasa ne sun rika raba tsakanin Naira 10,000 zuwa Naira 12,000 ga masu kada kuri’a da suka amince su zabi dan takarar gwamna da suke so.
Ya bayyana cewa a mazabar daya da biyu na ward hudu a St. Michael Nursery and Primary School, da wakilan sun lura da wadanda suka zabe su kafin su ba su kudin.
Wata mai kada kuri’a, Veronica Famigun da ke cikin jama’a, ta ce an dauki tsawon sa’o’i ana siyan kuri’u, inda ta bayyana farin cikinta kan yadda jami’an NSCDC suka tarwatsa wadanda ke yin wannan aika-aika.
Ta kuma jaddada bukatar jami’an tsaro su kara haskaka wasu rumfunan zabe a fadin jihar inda kuma za a iya aikata irin wadannan ayyuka.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, Muhammed ya fusata kan barazanar sayen kuri’u da ‘yan siyasa ke yi, inda ya ce mutanensa ba su da wani zabi da ya wuce su tarwatsa masu wannan sana’ar. Ya ce yana da kyau ‘yan kasa su fahimci cewa ya kamata a gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.