Rundunar soji ta kasa ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, inda suka kashe jami’an tsaro da dama da suka hada da sojoji da ‘yan sanda.
Rahotanni sun ce akalla mutane 43 da suka hada da sojoji 30 da jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma bakwai da fararen hula ne suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki wurin da ake hakar zinare.
Sun kuma yi awon gaba da wasu ‘yan kasar China.
Da take tabbatar da harin, rundunar sojin Najeriya a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce an kuma kashe wasu ‘yan bindiga a yayin harin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Rundunar GOC 1 ta koma wurin da za ta dauki nauyin gudanar da ayyukan da za a gudanar”.