Rundunar sojin sama ta ƙasa, ta kaddamar da wani samame mai taken ‘Operation Show no Mercy’ na fatattakar ‘yan ta’adda da ke dagula zaman lafiyar kasar ta hanyar hare-hare daban-daban.
Babban hafsan hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, yayin da yake kaddamar da farmakin a wani taro da kwamandojin rundunan ayyuka na NAF a gidajen kallo daban-daban ya hori sojojin sama da su tabbatar sun yi amfani da karfin wuta a kan ‘yan ta’addan.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Edward Gabkwet ya fitar a ranar Laraba cewa, hafsan hafsoshin ya gana da su a sansanin NAF da ke Kaduna a ranar Talatar da ta gabata sun hada da kwamandojin rundunar sojin saman da kuma kwamandojin rundunar sojin sama.
Amao ya ce, kaddamar da farmaki kan abokan gaba zai hana ‘yan ta’addar yancin walwala, ya kara da cewa hakan zai karawa jama’a kwarin gwiwa da tabbatar da zaman lafiya.


