Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a garin Yauri na jihar Kebbi a wani mataki na bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa.
Matakin na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin jihar Kebbi a ranar Alhamis.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.
Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne domin faɗaɗa ayyukanta zuwa sauran yankunan ƙasar, musamman domin samar da tsaro a kan iyakokin ƙasar na tudu da na ruwa domin magance ayyukan ɓata-gari a kogin Niger.
“Duk da irin muhimmanci da kogin Niger ke da shi wajen haɓaka ayyukan noma da samar da lantarki da kamun kifi da sauran sana’o’i, sannu a hankali ɓata-gari na mafani da shi wajen aiwatar da muggan ayyukansu”, in ji Nwatu.