fidelitybank

Rundunar soji ta yaye tsofafin ‘yan Boko Haram 500

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta ce. nan gaba za ta miƙa wasu tsoffin ‘yan Boko Haram sama da 500 da ta yaye, hannun hukumomin farar hula, bayan kammala horon raba su da tsauraran ra’ayi.

Ɗaruruwan tsoffin ‘yan Boko Haram ne suka yi rantsuwa a ƙarshen makonan. In ji BBC.

Gwamnatin Najeriya ce, ta ɓullo da shirin wanda sojoji ke gudanarwa a 2015, a wani ɓangare na dabarun yaƙi da ta’addanci.

‘Yan Boko Haram waɗanda bisa raɗin kansu suka ajiye makamai kuma suka miƙa wuya ga hukumomin ƙasar ne ke cin gajiyar wannan shiri na musamman, ciki har da samun horo kan sana’o’in hannu da sauya musu fahimta kan addini.

An ba su tallafin kyautata tunani da nufin sauke su daga tsattsauran ra’ayi, kafin a mayar da su cikin al’umma.

Babban jami’in kula da shirin mai taken ‘Operation Safe Corridor’, Birgediya Janar Joseph Maina ya ce tun bayan fara gudanar da shi, tsoffin ‘yan Boko Haram 1,070 ne tuni aka mayar cikin jama’a.

Da waɗannan tsoffin ‘yan Boko Haram da aka yaye a ƙarshen mako adadin waɗanda suka ci gajiyar horon ya ƙaru zuwa mutum 1,629.

Sai dai har yanzu akwai ɗari-ɗari daga ɓangaren al’umma ga tsoffin ‘yan Boko Haram ɗin, bisa la’akari da irin taɓargazar da ƙungiyarsu ta tafka.

Hukumomin Najeriya sun ce dubban ‘yan Boko Haram ne da iyalansu suka miƙa wuya tun bayan ɓullo da shirin.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp