Sufeto Janar na ‘yan sanda na ƙasa, Usman Baba ya amince da gudanar da taro na kwanaki uku ga manyan jami’an ‘yan sanda gabanin babban zabe na 2023.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce, taron wani bangare ne na kokarin da rundunar ke yi na tabbatar da zaman lafiya a cikin harkokin tsaron cikin gida da kuma samar da yanayi mai kyau don gudanar da babban zabe a shekarar 2023.
Taron mai taken ‘Muhimmancin tsarin dabarun ‘yan sandan Najeriya don gudanar da zabe cikin lumana’, za a yi shi ne tsakanin ranakun 18 zuwa 21 ga watan Oktoba a Imo.
Sanarwar ta ce, mahalarta taron za su kasance manyan jami’ai masu matsayi na mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda (DIG), mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda (AIG), kwamishinonin ‘yan sanda da sauran shugabannin rundunonin ‘yan sanda.
Ya kara da cewa sauran mahalarta taron za a zabo su a tsanake kan harkokin tsaro da gudanar da zabe a duk fadin duniya, domin su shiga nazari na takwarorinsu da kuma hada ra’ayoyi.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, za ta tabbatar da gudanar da ingantaccen tsaro kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe da kuma ba da dama ga manyan jami’ai su yi mu’amala da manyan jami’an ‘yan uwa na hukumomin tsaro da INEC da kuma abokan huldar ci gaban kasa da kasa.
Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shelanta bude taron tare da gabatar da jawabi. Gwamnoni da hafsoshin tsaro da shugabannin sauran hukumomin tsaro da sufeto-janar na ‘yan sanda na baya wasu baki ne da za su halarci taron.