Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP, Alkali Baba Usman, ya gargadi kasashen ketare kan gargadin ta’addanci a Najeriya.
Usman ya ce ya kamata kasashen ketare su daina sanar da jama’a game da fadakarwar ta’addanci.
Shugaban ‘yan sandan ya ce, sanarwar ta’addancin kwanan nan ya kamata a bai wa ‘yan sanda ba jama’a ba.
Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun fitar da sanarwar tsaro.
A cikin shawarwarin tafiye-tafiye, sun bukaci ‘yan kasar da su kaurace wa Abuja saboda hare-haren da ‘yan ta’adda suka shirya kai wa.
Sun kuma bukaci ‘yan kasar da su fice daga Abuja har sai an magance matsalar ta’addanci.
Sai dai IGP din ya baiwa jama’a tabbacin kare lafiyar su.
IGP ya yi wannan magana ne a ranar Asabar yayin da yake kaddamar da ofishin ‘yan sanda da bariki a Ibusa, karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta.
Ya ce, “Ta yaya za ku shiga kasar ku ce akwai sanarwar tsaro, ba ku sanar da ’yan sanda ba, kuna zagaya kuna gaya wa mutanen ku; kar ka je Abuja, ka dawo daga Abuja.
“Idan kana da bayanai kan tsaro, ya dace ka sanar da ‘yan sanda kuma za mu nemo hanyar da za mu magance shi, maimakon kai wa jama’a.
“Muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron mazauna.”