Dan wasan baya na kasar Jamus Antonio Rudiger ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid daga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kamar yadda kungiyoyin biyu suka tabbatar a ranar Alhamis.
Dan wasan mai shekara 29, wanda kwantiraginsa ya kare a Chelsea, ya kulla yarjejeniyar shekaru hudu a babban birnin Spain, Real ta sanar.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na intanet, Madrid ta ce, za a bayyana Rudiger a wani taron manema labarai a filin atisayen kungiyar a ranar 20 ga watan Yuni.
A halin yanzu yana tare da tawagar Jamus a jerin wasannin gasar UEFA Nations League, inda tawagar Hansi Flick za ta kara da Italiya a waje ranar Asabar sannan kuma za ta kara da Ingila da Hungary kafin kuma su kara da Italiya ranar 14 ga watan Yuni.