Dakarun Rapid Support Forces (RSF) da ke yaƙi da sojojin gwamnatin Sudan, sun zargi sojojin da ƙaddamar da hari ta sama kan tsohuwar fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum, babban birnin ƙasar.
Mazauna birnin sun ce, sun ji ƙarar bama-bamai a yankin, to amma sojojin sun musanta zargin.
Tsohuwar fadar shugaban ƙasar, wadda ke gaɓar tekun Nilu, a kusa da sabuwar fadar shugaban ƙasar ta yanzu.
Wakilan ɓangarorin biyu da ke faɗa da juna na wata tattaunawar sulhu a Saudiyya, to sai dai babu alamun ci gaba.
Yanayin da fararen hular da suka maƙale a birnin ke ciki na ci gaba da munana, yayin da likitoci ke gargaɗin cewa ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar na dab da durƙushewa.