Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya ce, gwamnatinsa ta gano wani jirgin sama 600 mallakin gwamnati da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Chibuike Rotimi Amaechi ya yi watsi da su a kasar Jamus.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya jagoranci tawagar shugabannin Rivers zuwa General Atomics Aerotec a Munich, Jamus.
A cewar Wike, an gano jiragin ne ta hanyar leken asiri, inda ya kara da cewa, jiragen da aka siyo a shekarar 2003, an yi watsi da su ne a kasar ta Turai tun shekara ta 2012 ba tare da wani bayani ba.
Wike, yayin da yake bayyana matakin da gwamnatin da ta shude ta dauka a matsayin wanda bai dace ba, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe sama da Yuro miliyan 3 wajen gyara da kuma dawo da jirgin.
“Lokacin da muka shiga ofishi a shekarar 2015, ba mu taba tunanin cewa, jirgin namu ya na wurin ku ba. Ya kasance batun yin tambayoyi ne kafin mu samu labarin cewa, Legacy 600 mallakar jiharmu su na RUAG, kafin Janar Atomics.
Wike ya godewa hukumomin Jamus da suka amince da daukarsu ta hanyar kwato jirgin da kuma rashin boye komai daga gwamnatin jihar Rivers.
“Gwamnatin Dokta Peter Odili ce ta sayo wannan jirgi a shekarar 2003, kuma a shekarar 2007, ya mika shi ga gwamnati mai zuwa, wadda ita ce ta magabaci, a yanzu, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi. Yayin da yake mulki, a shekarar 2012, an kawo wannan jirgin nan. Dalilan da ba mu sani ba,” ya kara da cewa.
“Batun shine, me yasa babu wani takardu, domin sanar da gwamnati mai zuwa cewa, an aika da jirgin zuwa RUAG domin dubawa?” Wike ya tambaya.