Birmingham City ta nada Wayne Rooney a matakin sabon kociyanta.
Tsohon dan wasan tawagar Ingila, mai shekara 37 ya koma kungiyar da ke buga gasar Championship kan yarjejeniyar kaka uku da rabi.
Rooney ya maye gurbin John Eustace, wanda aka kora ranar Litinin, bayan wata 15 da ya ja ragamar Birmingham.
Wannan shi ne nadin farko da sabon wanda ya mallaki kungiyar dan kasar Amurka mai kamfanin Shelby Comanies Limited ya yi tun bayan da ya karba a watan Yuli.
Rooney zai yi aiki tare da mataimaki, tsohon dan wasan United Ashley Cole, wanda shi ne mataimakin mai horar da matasan Ingila ‘yan kasa da shekaru 21.
Haka kuma John O’Shea shima zai tallafa Rooney, wanda shi ne mai horar da tawagar kwallon kafa ta Jamhuriyar Ireland.
Haka kuma Carl Robinson da Pete Shuttleworth za su yi aiki da Rooney a Birmingham, wadanda suka taimaka masa a DC United.
Wannan shi ne karo na uku da Rooney zai horar da kungiya, bayan kungiyar da take buga MLS da kuma Derby County.
Zai fara jan ragamar wasan farko ranar 21 ga watan Oktoba da zai fuskanci Middlesbrough