Dan wasan gaba na Manchester United, Cristiano Ronaldo ya amince cewa, zai ci gaba da zama a ƙungiyar a wannan bazarar.
A baya dai kyaftin din Portugal din yana yunkurin ficewa daga Old Trafford, duk da cewa sayen tsohon abokin wasansa Casemiro daga Real Madrid ya haifar da koma baya a shawararsa.
Gaba daya dai, Man United ta dage cewa dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ba na sayarwa bane kuma ya ci gaba da zama a cikin shirin kocin Erik ten Hag kuma da alama Ronaldo ya amince da shan kaye.
A cewar kwararre kan harkokin wasanni na kasar Portugal, Pedro Almeida, Ronaldo ya amince zai zama dan wasan Man United a kakar wasa ta bana.
Almeida ya rubuta a shafin Twitter a safiyar Lahadi: “Cristiano ya yarda ya ci gaba da zama a @ManUtd. #Isowar Casemiro yana da mahimmanci ga yanke shawara. Wannan shine bayanin!”


