‘Yan sanda sun gargadi dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo bayan da ya fasa wayar wani yaro mai cutar Autistic.
Lamarin ya faru ne bayan da Red Devils ta sha kashi a hannun Everton da ci 1-0 a kakar wasan da ta wuce.
Ronaldo ya bayyana ya bugi hannun Jacob Harding yayin da yake barin filin wasan bayan da suka sha kashi.
Daga baya ya nemi gafarar matashin mai shekaru 14, amma ‘yan sanda sun yi hira da shi cikin taka-tsan-tsan dangane da wani hari da ake zarginsa da aikatawa.
Wata sanarwa da ‘yan sandan Merseyside suka fitar a ranar Laraba, ta ce: “Za mu iya tabbatar da cewa wani mutum mai shekaru 37 ya halarta bisa radin kansa kuma an yi masa tambayoyi cikin taka-tsan-tsan dangane da zargin cin zarafi da lalata. Zargin na da alaka da wani lamari da ya faru bayan wasan kwallon kafa na Everton da Manchester United a Goodison Park a ranar Asabar 9 ga watan Afrilu.
“An magance lamarin ta hanyar taka tsantsan. Yanzu dai an kammala maganar.”
An fahimci cewa dan wasan mai shekaru 37 ya amince ya biya diyya ga Harding.


