An bayyana wani tsohon dan gwagwarmayar hada-hadar wasan dambe na Martial Arts (MMA), Goncalo Salgado, a matsayin mai tsaron lafiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo.
Ronaldo na daya daga cikin ’yan wasa da aka fi sani da su a duniya, don haka yana bukatar wani babban jami’in tsaron da zai kare kansa da iyalansa.
Salgado, asalinsa daga wani gari kusa da Lisbon, wanda aka sani da Seixal, yana tsaye a 6-foot-2.
Salgado ya fafata ne a rukunin masu nauyi na MMA kuma yana da tarihin kwarewa na nasara bakwai da asara biyu.
Bayan ya yi nasara a fafatawa biyar na farko, dan kasar Portugal ya sha kashi na farko da Zilong Zhao a shekarar 2007.
Salgado ya koma zobe inda ya doke Frederic Sinistra da Akim Asinine.
Ya daina fada a 2011 bayan Arsen Abdulkerimov ya doke shi, kuma ya yi ritaya a 2014.
Kwararren mai horar da jami’an tsaro yana aiki a matsayin mai tsaron sirri ga Cristiano Ronaldo.