Kyaftin din Al-Nassr, Cristiano Ronaldo, ya mayar da martani kan wasan da kungiyarsa ta yi a Saudi Pro League da ta doke Al-Ta’ee da ci 2-0 a ranar Talata.
Fenaretin da Ronaldo ya ci da Talisca ya tabbatar da cewa Al-Nassr ta doke Al-Ta’ee a filin wasa na Prince Abdul Aziz bin Musa’ed.
Da yake mayar da martani, Ronaldo, a wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Instagram bayan kammala wasan, ya bayyana nasarar da suka samu a kan Al-Ta’ee a matsayin muhimmiyar nasara, inda ya bukaci abokan wasansa da su ci gaba da imani har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
Tsohon dan wasan na Manchester United ya ce: “Nasara mai mahimmanci a daren yau, sauran wasanni 3 a gaba! Muna ci gaba da yin imani har zuwa ƙarshe!”
Nasarar da aka yi kan Al-Ta’ee na nufin Al-Nassr tana matsayi na biyu a kan teburin gasar Saudi Pro League da maki 60 a wasanni 27.
Ronaldo dai zai yi fatan ci gaba da bajintar da yake yi wa Al-Nassr idan za su karbi bakuncin Al-Shabab a mako mai zuwa.