Dan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo, ya koma atisaye tare da sauran abokan wasansa na kungiyar, bayan hukuncin da Erik ten Hag ya yi masa.
A makon da ya gabata ne kocin ya nemi ya koma atisaye shi kadai, a wani bangare na jan kunnen da aka yi masa.
Ronaldo mai shekara 37, ya ki shiga wasan da United da ta buga da Tottenham a ranar Larabar da ta gabata saboda an ajiye shi a benci, sannan kuma aka ki amfani da shi a wasan da Manchester United ta yi 1-1 da Chelsea.
Ten Hag ya ce bayan wannan hukunci ba wanda za a kara yi masa.
An gano cewa Ronaldo da Ten Hag sun tattauna a cikin wannan kwanakin.


