Sabon dan wasan Al-Nassr, Cristiano Ronaldo, ya shirya tsaf domin fara taka leda a kungiyar yayin da yake shirin buɗe sabon babi a fagen kwallon kafa.
Ronaldo ya koma Al-Nassr ne a matsayin dan wasa kwanaki kadan da suka gabata bayan da aka soke kwantiraginsa da Manchester United a watan Nuwamban bara.
Kyaftin din na Portugal ya ba da labarin komawarsa kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya.
Dan wasan mai shekaru 37 a halin yanzu yana zaman dakatarwar wasanni biyu, saboda lokacin da ya fasa wayar wani magoyin bayan Everton daga hannunsa a lokacin da yake barin filin wasa a Goodison Park a bara.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Asabar, Ronaldo ya saka hotonsa na atisaye tare da taken: “Ku sanya kowane motsa jiki ku ƙirga.”
Wasa biyu na gaba na Al-Nassr zasu fafata ne da Al-Shabab da Ettifaq a ranakun 14 da 22 ga watan Janairu.