Dan wasan gaban Portugal, Diogo Jota, ya yi ikirarin cewa, yana gwada kansa da Cristiano Ronaldo a matsayin mai ƙara masa kwarin gwiwa don shawo kan matsalar zura kwallo a raga a Liverpool.
Har yanzu Jota bai ci wa Liverpool kwallo ko daya ba a kakar wasa ta bana, bayan da ya rasa mafi yawan ta sakamakon matsalar kaka.
Dan wasan ya buga wa Reds jimillar wasanni 19 a kakar bana amma har yanzu bai bude asusunsa ba.
Duk da cewa dan wasan na Portugal ya taimaka sau bakwai, amma ya dage cewa ya mayar da hankali sosai kan wasansa.
Jota, abokin wasan Ronaldo a cikin tawagar kasar Portugal, ya shaida wa talkSPORT “A gaskiya abin ban haushi ne.”
Ronaldo ya taba jimre tsawon watanni 16 ba tare da cin kwallo ba tare da tawagar Portugal a shekarar 2010.
“Na taba jin labari, kuma tabbas Ronaldo bai buga wasanni 30 ba, amma ya yi wasanni da dama ba tare da ya zura kwallo a raga ba, kuma mutane suna tambayarsa.
“Ya kasance yana cewa kusan kamar ketchup ne. Lokacin da ɗigon farko ya fito, komai ya fito don fatan haka lamarin yake a gare ni. “