fidelitybank

Ronaldo ba zai buga wasan Najeriya ba

Date:

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ba zai haska a wasan sada zumuncin shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da za a fafata tsakanin Najeriya da kasarsa a wannan Alhamis ɗin ba.

A cewar kocinsa Fernando Santos, ɗan wasan tun jiya bai fito atisaye ba, kuma yana bukatar hutu na ɗan wani lokaci.

A wannan makon ne Ronaldo mai shekara 37 ya caccaki kungiyar Manchester United a wata hira da aka yi da shi, inda ya ke nuna cewa ba ya darajar kocinsa, Erik ten Hag saboda abubuwan da yake yi masa.

Sannan ya nuna cewa United ba ta yi masa adalci ba, kuma akwai ‘yan wasan da ba sa farin cikin kasancewarsa a kungiyar.

Idan Ronaldo ya warke ana sa rai ya haska a karo na biyar a gasar cin kofin duniya, babu mamaki kuma ta karshe ga ɗan wasan.

Portugal za ta yi fafatawar farko ne da Ghana a ranar 24 ga watan Nuwamba, kafin daga bisani su haɗu da Uruguay da kuma Koriya Ta Kudu.

Ɗan wasan da kasarsa Portugal ba su taɓa lashe kofin duniya ba, amma sun taka rawar gani a gasar cin kofin Turai ta 2016 da kuma lashe League a 2019.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...
X whatsapp