Romaniya ta kira jakadanta gida daga Kenya kuma ta nemi afuwa bayan ya kwatanta ‘yan Afirka da birai.
Dragos Tigau ya yi kalaman ne yayin wata ganawa a wani ginin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Nairobi ranar 26 ga watan Afrilu.
A cewar kamfanin labarai na AFP, Mista Tigau ya ce “tawagar Afirka ta shigo cikinmu” lokacin da ya hango wani biri ta taga.
Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Kenya, Kamau Macharia, shi ne ya fara fito da kalaman na Tigau a ranar Alhamis.
A ranar Asabar Romaniya ta sanar cewa sai a wannan makon aka sanar da ita abin da ya faru kuma “ta fara shirin kiran jakadan nata zuwa gida”.