Hukumar kashe gobara ta Isra’ila ta ce sama da tawaga talatin ce ke fafatawa da gobarar daji da ta tashi cikin dare a yankin arewacin ƙasar.
Gobarar ta tashi ne sakamakon makaman roka da ƙungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba.
Kungiyar ta ce harin na ramuwar gayya ne kan harin da jirage marassa matuka na Isra’ila suka kai kan wasu motoci a kudancin kasar Labanon wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wani mutum daya. In ji BBC.