Babban mai horar da ‘yan wasan Jamhuriyar Benin, Gernot Rohr ya bayyana jerin ‘yan wasa 25 da za su buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA a shekarar 2026 da Rwanda da Najeriya.
Rohr wanda a baya ya jagoranci Super Eagles ya bayyana sunayen ‘yan wasa 19 da ke kasar waje da kuma tauraro guda shida a cikin tawagar.
Gogaggen dan wasan gaba Steve Mounie, ‘yan wasan biyu haifaffen Najeriya, Ayegun Tosin da Samson Akinyoola na cikin ‘yan wasan da kocin dan kasar Jamus ya lissafa.
Squirrels ba su da nasara a rukunin C kuma dole ne su yi nasara a wasanni biyu masu zuwa don haɓaka damar samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya a karon farko.
Tawagar Rohr za ta karbi bakuncin shugabannin rukunin C Amavubi na Rwanda a filin wasa na Felix Houphouet Boigny ranar Alhamis 6 ga watan Yuni.
Haka kuma za su nishadantar da makwabta, Najeriya a wuri guda bayan kwanaki hudu