Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi kira ga Hukumar Tattara Haraji da Kudi, RMAFC, da ta yi la’akari da bayar da karin bayani ga ‘yan Najeriya kan bambancin albashi da alawus-alawus na ‘yan majalisa.
Gbajabiamila ya yi wannan rokon ne a ranar Alhamis a Abuja lokacin da ya karbi bakwancin tawagar RMAFC a majalisar dokokin karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Mohammed Bello Shehu.
Shugaban majalisar ya lura cewa cece-kucen da ake yi kan batun biyan ‘yan majalisar dokoki da mayar da shi muhawara a bainar jama’a a kodayaushe ya samo asali ne, sakamakon dunkulewar albashi da alawus-alawus na ‘yan majalisar tare.
A cewar Gbajabiamila, alawus-alawus na da nasaba da ayyuka ko aiki na ofishin dan majalisa kamar kula da ofishin mazabar, yayin da albashin shi ne ainihin albashin da yake samu a matsayinsa na dan majalisa.
“Ya kamata ku bayyana wa jama’a bambancin albashi da alawus-alawus. Albashi ya bambanta kuma ana nufin alawus don wasu batutuwa masu yawa.
“Wannan bayanin ya kamata ya kasance wani bangare na abin da kuke aiki akai a yanzu game da bangaren shari’a da masu rike da mukaman siyasa”, in ji shi.
Ya kuma shawarci RMAFC da ta gina cibiyar sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin kudaden shiga a dukkan hukumomin da ke samar da kudaden shiga na gwamnati, yayin da ya bukaci ta gabatar da cikakken bayani kan bukatunta domin baiwa majalisar damar yin aiki da ita cikin gaggawa.


