Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 cikin su 32 sun fice daga Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa APC.
Ƴan majalisar dokokin sun sanar da matsayarsu ne a wani taro da suka yi yau Litinin.
An kuma ga wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta inda yan majalisar ke ɗauke da tutar APC.
Sun ce babban dalilin da ya sa suka sauya sheƙa shi ne rarrabuwar kan da aka samu a jam’iyyar PDP.
Lamarin dai ya ƙara zafafa rikici tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin da ke yi wa tsohon gwamna Nyeson Wike mubaya’a.