Babban alkalin alkalai kuma kwamishinan shari’a na jihar Ribas, Zacchaeus Adangor, ya yi murabus daga ofishin sa.
Wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
A cikin wasikar, Adangor ya ce murabus din nasa ya dogara ne kawai akan wasu dalilai na kansa.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa murabus din na iya rasa nasaba da rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.