fidelitybank

Rikicin Ukraine: Rasha ta magantu a kan Amurka

Date:

Kasar Rasha ta ce ba ta da kwarin gwiwa bayan tattaunawar farko da Amurka kan rikicin Ukraine, kuma ba za ta bari bukatunta na tabbatar da tsaro daga kasashen Yamma su shiga tsaka mai wuya a tattaunawar ba.

Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce, yan a da kyau a ce an gudanar da tattaunawar da aka yi a ranar Litinin a birnin Geneva a fili, mai ma’ana kuma kai tsaye, amma Rasha na da sha’awar samun sakamako kawai.

Kasar Rasha ta tura kasashen yammacin duniya kan teburin tattaunawa ta hanyar tattara sojoji a kusa da kan iyakar kasar ta Ukraine, yayin da ta ke matsa lamba kan wasu bukatu masu nisa da za su hana Ukraine shiga kungiyar tsaro ta NATO da kuma dawo da fadada kawancen shekaru ashirin a Turai.

Amurka ta ce, ba za ta iya amincewa da wadannan bukatu ba, ko da ya ke a shirye ta ke ta shiga cikin wasu bangarori na shawarwarin na Rasha, ta hanyar tattaunawa kan batun tura makamai masu linzami ko iyaka kan yawan atisayen soja.

Sai dai kuma Dimitry Peskov, ya ce lamarin zai kara fitowa fili bayan zagaye na biyu na tattaunawa da Rasha za ta yi a wannan makon tare da kungiyar tsaro ta NATO a Brussels a yau Laraba da kuma kungiyar tsaro da hadin gwiwa a Turai (OSCE) a birnin Vienna na kasar Austria ranar Alhamis.

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp