fidelitybank

Rikicin Ukraine: Rasha ba za ta taɓa ƴan Najeriya ba a Ukraine – Alexei Shebarahin

Date:

Jakadan ƙasar Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa da gwamnatin tarayya cewa, Rasha ba za ta taɓa ƴan Najeriya ba a rikicin da ke ƙara yin tsanani tsakanin kasar Rasha da Ukraine.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya samu damar ganawar sirri da jakadan ya shaida wa Shebarshin cewa, Najeriya kawar Rasha ce.

A cewar Onyeama, yayin tattaunawa da Shebarshin, ya sanar da shi cewa, Najeriya ba za ta lamunci cin zarafin ƙasa da ƙasa ba daga wata ƙasar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ƙasar da ke da jakada a Najeriya.

Sai dai Jakadan ya ce, Rasha ba ta kai wa farar hula farmaki, kuma ba za su bari a cutar da Najeriya ba kuma sojojinsu za su tabbatar sun kula. Hasali ma ba sa kai farmakin bangaren farar hula.

“Wannan ne matsayar gwamnatin tarayya kuma muna da ‘yan Najeriya guda 5,600 a Ukraine, kuma hankalin mu a tashe yake, musamman ganin bama-baman da ake aunawa Rasha. Gwamnatin Najeriya ta na shirin zuwa ƙwaso ‘yan kasar”. In ji Onyeama.

A martanin Jakadan Rasha a Ukraine, ya ce, zai yi wa shelkwatar su magana, kuma alamu sun nuna cewa, suna da alaka mai kyau da Najeriya. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito.

latest news 
in nigeria today 2021 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp