Fadar Kremlin ta ce shugaban Rasha Vladimir Putin ba zai gudanar da taron manema labarai na karshen shekara ba a wannan shekara.
Gidan talabijin na Al Jazeera ya ba da rahoton cewar, mai magana da yawun fadar ta Kremlin, Dmitry Peskov, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya kuma lura cewa Shugaba Putin “yana magana akai-akai ga manema labarai, gami da ziyarar kasashen waje”.
Sai dai bai bayar da dalilin kin gudanar da taron manema labaran ba, wanda yakan dauki tsawon sa’o’i da dama ya na ganawa da ‘yan jaridu.
Masu lura da al’amuran yau da kullum, na kallon matakin a matsayin yakin da Rasha ke yi da Ukraine, wanda ya fara a watan Fabrairu.
Vladimir Putin, wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 2000, ya gudanar da taron manema labarai a cikin watan Disamba mafi yawan shekarun mulkinsa, lamarin da ya yi amfani da shi wajen haska hotonsa a gidan talabijin na kasar.
Dakatar da taron manema labarai na bana ya zama karo na farko a cikin shekaru goma da Putin ba zai gudanar da bikin na Disamba ba, wanda wata dama ce da ba kasafai ake samu ba ga manema labarai a wajen fadar Kremlin, ciki har da ‘yan jaridu na kasa da kasa, su yi wa shugaban Rasha tambayoyi kai tsaye.
Yakin da sojojin Rasha suka fara a kasar Ukraine ya zama abin tattaunawa a duniya, inda kasashen yammacin duniya ke kallonsa a matsayin wani mataki na tada kayar baya ga kasar Ukraine, don haka ya ci karo da jerin takunkumin karya tattalin arziki kan Rashan da ta mamaye kasar.