Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya sake gargadin cewa akwai hatsarin rikicin Ukraine na iya kai wa ga Yaƙin Duniya na Uku, amma ya ce yana sa ran za a kawo karshensa da yarjejeniyar zaman lafiya.
Da yake magana da kafafen yada labaran kasar Rasha, ya ce Moscow na son kaucewa abin da ya kira hadarin wucin gadi na irin wannan rikici.
Mista Lavrov ya zargi NATO da shiga yakin, yana gargadin cewa kasarsa za ta kai wa tawagar kungiyar da ke kai makamai Ukraine hari ba kakkutawa.
Makonni kadan da suka gabata shugaba Putin ya umarci dakarunsa na nukiliya su kasance cikin shiri.
Amurka ta ce ba ta son shiga rikicin ta hanyar sanya sojojinta a ciki. domin hakan na iya haifar da yakin duniya na uku.