Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya buƙaci ƙungiyar Tarayyar Turai da ta gaggauta amincewa da kasarsa a matsayin mambar ƙungiyar Tarayyar Turai.
A cikin sanarwar ta bidiyo Zelensky ya kuma bukaci sojojin Rasha da su ajiye makamansu.
“Manufarmu ita ce mu kasance cikin ƙasashen Turai, kuma mafi mahimmanci, mu kasance a kan daidaito. N tabbata yana yiwuwa,” in ji shi.
“Ku watsar da kayan aikinku, ku fice, kada ku yarda da kwamandojinku, kada ku yarda da masu yada farfaganda, ku ceci rayukanku,” in ji shi.
“Mun dauki wannan matakin da ba shi da sauki, amma mai amfani ta fuskar tsaronmu,” inji shi.
Shugaban na Ukraine ya kuma ce, za su saki waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa masu kwarewar yaƙi domin su taimaka wajen kare kasar.