Kungiyar matasan Neja Delta (NDYC), ta bukaci a gaggauta sakin Hon. Dagogo Fara, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Degema/Bonny na jihar Rivers a karkashin jam’iyyar PDP.
An kama Dagogo ne kwanaki kadan da suka gabata a Fatakwal, yayin da yake gudanar da tantancewar neman kujerar gwamna.
Ƴan sanda sun kama Dagogo Fara wanda kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PPD a jihar Ribas ne, bisa umarnin gwamnan jihar, Cif Nyesom Wike, bisa zargin daukar ’yan kungiyar asiri su kai hari sakatariyar PDP a Fatakwal.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a bayan ya jagoranci zanga-zangar zuwa ofishin babban sufeton ‘yan sanda, majalisar dokoki da ma’aikatar shari’a kan ci gaba da tsare Hon Fara Dagogo, kodinetan NDYC na kasa, Kwamrade Jator Abido da shugaban babban birnin tarayya, Kwamrade Adam Ogomugo Margo, sun dage cewa dole ne a yi adalci ba tare da bata lokaci ba.