Rikicin jam’iyyar APC reshen jihar Gombe na ƙara kamari, wanda lamarin ya fara shafar gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya.
Mai bada shawara na musamman kan harkokin gwamnati ga gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jigar Gombe, Alhaji Garba Jijji Gadam, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Daily Trust ta rawaito cewa, tsohon hadimin gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne, bisa ra’ayin kansa, kuma ya ajiye mukaminsa nan take ba tare da ɓata lokaci ba.
Hadimin gwamna mai bada shawara kan harkokin gwamnati, Jijji Gadam. ya yi murabus daga muƙaminsa nan take.
Gadam ya ce, ya ɗauki wannan matakin ne, domin sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa, amma bai faɗi inda ya dosa ba.